Mutane biliyan 4 na iya yin kiba fiye da kima nan da shekaru 12 - Rahoto
An yi hasashen cewa yawan mutanen da za su yi kiba fiye da kima za su kai biliyan 4 nan da shekaru 12, kana tasirin hakan a kan tattalin arziki zai kai dala tiriliyan 4 da biliyan 32 duk shekara daga shekarar 2035 idan ba aa dauki matakan waraka da kariya ba.
Wallafawa ranar:
Wannan tasirin ya kai kaso 3 na jimillar kudaden shiga na duniya baki daya, kuma ana iya kwatanta shi da na annobar Covid 19 a shekarar 2020.
Wani rahoton da mujallar Obesity Atlas ta wallafa ta ce akasarin al’ummar duniya – kaso 51 ko sama da mutane biliyan 4 za su yi kiba fiye da kiman zuwa shekarar 2035, wato mutum 1 cikin mutane 4 zai fuskanci kalubalen kiba fiye da kima.
Rahoton ya nuna cewa kasashen marasa karfin tattalin arziki ne suka fi fuskantar wannan matsala ta kiba fiye da kima, zalika, 10 daga cikin kasashen da ke fama da wannan matsala, 9 kasashe ne matalauta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu