Isa ga babban shafi

Mutane sama da 20 ne suka mutu saboda tsananin sanyi a Amurka

Fiye da Amurkawa 200,000 ne suka wayi gari ba tare da wutar lantarki ba a safiyar ranar Kirsimeti sakamakon guguwar sanyi da ta shafe kwanaki ana tafkawa a wasu jihohin gabashin Amurka, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 20.

Yadda ruwa ya mamaye gidaje a Massachusetts yayin da wata guguwar sanyi ta afkawa gabar tekun gabashin Amurka
Yadda ruwa ya mamaye gidaje a Massachusetts yayin da wata guguwar sanyi ta afkawa gabar tekun gabashin Amurka GETTY IMAGES NORTH AMERICA/AFP
Talla

Matsanancin sanyi, dauke da guguwa mai cike da tarihi ya mamaye  jihohin Amurka 48 a wannan makon, abin da ya haifar da cikas ga matafiya da dakatar da zirga-zirgar dubban jirage, inda dubban gidaje ke cike da dusar kankara.

An tabbatar da mutuwar mutane 22 a jihohi takwas, ciki har da akalla mutane bakwai da suka mutu a yammacin New York, inda dusar kankara dauke iska mai tsanani suka mamaye garuruwa.

Shugaban gundumar Mark Poloncarz ya shaida wa manema labarai cewa, "Muna da mutane bakwai da aka tabbatar sun mutu sakamakon guguwar da ta afku a gundumar Erie.

Wasu ma'aurata a Buffalo, wanda ke kan iyaka daga Canada, sun shaidawa AFP cewa tsananin sanyi ba zai basu damar tafiyar tsawon minti 10 ba na ziyartar danginsu a bikin Kirsimeti.

Haka zalika matafiya sun kasance a makale a filayen jirgin saman a Atlanta, Chicago, Denver, Detroit, Minneapolis da New York.

Kankara da ta mamaye kan titi ta haifar da rufe wasu hanyoyin zirga-zirgar ababen hawa na wucin gadi da suka hada da ta Interstate 70.

Hukumomin kasar dai sun gargadi direbobi da kada su bi hanyoyin daidai lokacin da al’ummar kasar kan ganiyar zirga-zirga saboda bukukuwan Kirismeti.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.