Isa ga babban shafi

Amurka ta tsare wani dan kasar Libya da ake zargi da harin Lockerbie a 1988

Wani mutum dan kasar Libya da ake zargi da kera bom din da ya lalata jirgin Pan Am a 1988, yanzu haka yana tsare a hannun Amurka.

mutum 270 ne suka mutu sakamakon harin da aka kai kan jirgin
mutum 270 ne suka mutu sakamakon harin da aka kai kan jirgin AFP/Archivos
Talla

Ma’aikatar tsaron Amurka ta ce an tsare Abu Agila Muhammad Masud Kheir Al-Marimi, wanda hakan ke tabbatar da sanarwar da masu shigar da kara a Scotland suna fitar.

Amurka ta ce Masud zai bayyana a gaban kotun Columbia da ke kasar, amma bata bayyana ranar da zai gurfana ba.

Bayan wani bincike na hadin gwiwa na shekaru uku da Dumfries da Galloway Constabulary da hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka (FBI) suka yi, an bayar da sammacin kama wasu ‘yan kasar Libya biyu a watan Nuwamba 1991.

A shekara ta 1999, shugaban Libya Muammar Gaddafi ya mika mutanen biyu domin yi masu shari’a a Camp Zeist, na kasar Netherlands, bayan da aka dauki tsawon lokaci ana tattaunawa da kuma takunkumin Majalisar Dinkin Duniya.

A shekara ta 2001, aka daure Abdelbaset al-Megrahi, wani jami'in leken asiri na kasar Libya hukuncin daurin rai da rai bayan an same shi da laifuffuka.

A watan Agustan 2009, gwamnatin Scotland ta sake shi bisa dalilai na afuwa bayan an gano yana dauke da ciwon daji na hanji. Ya mutu a watan Mayun 2012 a matsayin mutum daya tilo da aka yankewa hukunci kan harin.

A shekara ta 2003, Gaddafi ya karbi alhakin harin Lockerbie da ‘yan kasarsa suka kai, kuma ya biya diyya ga iyalan wadanda abin ya shafa, ko da yake ya ci gaba da cewa bai taba bayar da umarnin kai harin ba.

Yarda da alhakin na daga cikin jerin sharuddan da wani kuduri na Majalisar Dinkin Duniya ya gindaya na dage takunkumin da aka kakabawa Libya. Libya ta ce dole ne ta karbi alhakin saboda matsayin Megrahi a matsayin ma'aikacin gwamnati.

A ranar 11 ga Disamba, 2022, hukumomin Scotland suka ba da sanarwar cewa Masud yana hannun Amurka. A watan da ya gabata ne aka ruwaito cewa, wasu gungun ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Masud a Libya, lamarin da ya sa ake kyautata zaton za a mika shi ga hukumomin Amurka domin gurfanar da shi a gaban kuliya.

Dukkanin fasinjojin jirgin 243 da ma'aikatan jirgin 16 ne suka mutu.

Daga cikin jimillar 270 da suka mutu, 190 ‘yan Amurka ne sai 43 ‘yan Burtaniya.

An kashe mazauna Lockerbie 11 a Sherwood Crescent lokacin da wani sashen jirgin ya bugi wani gida mai lamba 13 Sherwood Crescent.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.