Isa ga babban shafi

Kafofin yada labaran Turai 'yan amshin shata ne - Putin

Shugaba Vladimir Putin ya ce rabin 'yan kasar Rasha da aka kira zuwa aikin soja a watan Satumba an tura su zuwa Ukraine.

Shugaba Vladmir Putin na Rasha
Shugaba Vladmir Putin na Rasha REUTERS/Alexander Nemenov/Pool
Talla

Shugaban ya ce daga cikin sojoji 300,000 da aka dauka aiki, an tura 150,000 fagen daga.

Mista Putin wanda ya bayyana hakan yayin wata ganawa da kwamitinsa da ke kare hakkin bil’adama, wanda aka nuna a gidan talibijin din kasar, ya ce yanzu haka 77,000 daga cikin sojoji na cikin shirin ko ta kwana.

Rashad ai ta zargi Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin kasa da kasa da kuma kafafen yada labaran yammacin duniya da kokarin bata mata suna.

“Bayan mun aike da sojoji zuwa Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu, Kungiyoyin kare hakkin bil'adama na Majalisar Dinkin Duniya, Majalisar Turai da sauran wuraren kare hakkin "sun fara nuna mana kyamarsu", in ji Putin.

Ya kuma zargi kafofin yada labaran kasashen waje da yada "labaran karya" game da yakin da Moscow na soja ke yi a Ukraine.

Shugaba Vladimir Putin wanda ya sha alwashin yin amfani da dukkan hanyoyin soji wajen kare kasar Rasha, Moscow za ta yi amfani da makaman nukiliya a matsayin martani ga harin da abokan gaba suka kai musu.

"Lokacin da aka kawo mana hari, sai mu mayar da martani," a cewar Putin lokacin da yake shaida wa taron kwamitinsa na kare hakkin bil'adama, yana mai jaddada cewa dabarun kasarsa ya dogara ne kan manufar "abin da ake kira aikin ramuwar gayya".

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.