Isa ga babban shafi

Masu kai hari kan Zaporizhzhia mahaukata ne - MDD

Shugaban Hukumar da ke Sanya Ido kan Nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya,  ya yi tur da hare-haren da ake kaddamarwa kan tashar nukiliya ta Zaporizhzhia wadda Rasha ta mamaye a Ukraine, inda ya bukaci a kawo karshen wannan al’amari da ya bayyana matsayin hauka, yayin da kasashen biyu ke ta zargin juna.

Tashar nukiliyar Zaporizhzhia da Rasha ta kwace daga hannun Ukraine.
Tashar nukiliyar Zaporizhzhia da Rasha ta kwace daga hannun Ukraine. © REUTERS/Alexander Ermochenko
Talla

A cikin wata sanarwa da ya fitar, shugaban Hukumar da ke sanya ido kan nukiliya ta duniya , Rafael Grossi ya ce, labaran da suke samu na tayar musu da hankali, kuma a cewarsa, ba za su taba amincewa da fashe-fashen abubuwa ba a babbar tashar nukiliyar.

Shugaban ya kuma ce dole ne a gaggauta kawo karshen wannan al’amari kamar yadda ya yi ta nanatawa a can baya.

A daren Asabar wayewar garin jiya  Lahadi, an samu gomman fashe-fashen abubuwa a tashar nukiliyar, kuma  tawagar Hukumar da ke Sanya Ido kan Nukiliyar ta ce, ta shaida lamarin kamar yadda sanarwar ta fadi.

Grossi ya ce, ba a cikin kuskure aka kaddamar da jerin hare-haren ba kan tashar nukiliyar ta Zaporizhzhia, domin kuwa da gan-gan aka yi haka.

Yanzu haka dai, hukumar za ta tura wata tawagar kwararru zuwa wannan tasha wadda ita ce mafi girma a nahiyar Turai, kuma tana ci gaba da kasancewa a hannun sojojin Rasha da suka mamaye ta.

A bangare guda, Ukraine  ta yi watsi da zargin da Rasha ta yi mata na cewa, ta kashe mata sojojinta da suka mika wuya bayan sun ajiye makamansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.