Isa ga babban shafi

Kotun Bolivia ta daure tsohuwar shugabar kasar Jeanine Anez gidan yari

A Bolivia, kotu ta zartas da hukuncin dauri na shekaru 10 ga tsohuwar shugabar kasar Jeanine Anez bisa tuhumar ta da hada  baki a juyin mulki yan lokuta da murabis  na tsohon Shugaban kasae Eva Morales da ya shugabanci kasar kama daga shekara ta 2006 zuwa 2019.

Jeanine Añez, Tsohuwar Shugabar kasar Bolivia
Jeanine Añez, Tsohuwar Shugabar kasar Bolivia © AFP - Presidência da Bolívia
Talla

Jeanine Anez mai shekaru  54 ta sabi ragamar shugabancin wannan kasa  a watan nuwamba na shekara ta 2019 yan lokuta bayan murabis na Eva Morales,wanda zanga-zangar jama’ar kasar ta tilastawa sauka daga karagar mulki.

Ana zargin Tsohon Shugaban kasar Eva Morales da gazawa wajen tafiyar da harakokin gwamnati,rashawa da talauci sun haddabi jama'r kasar ta Bolivia.

Al'amarin da ya fusata jama'ar Bolivia ga zanga-zanga.

'Yar Majalisar Dattijai ta sanar da hawa Shugabancin Bolivia

Wakiliya a Majalisar dattawan Bolivia ta sanar da itace sabuwar shugaban kasar bayan da Evo Morales ya ajiye shugabancin, ya kuma tsere zuwa Mexico don samun mafakar siyasa.

Alkalai masana dokokin sun bayyana cewa  shugabantar kasar da Jeanine Anez ta yi,ya sabawa kudin tsarin mulki,tamkar juyin mulki ne,sai dai tsohuwar shugabar kasar ta bayyana cewa zata daukaka kara .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.