Isa ga babban shafi
Venezuela - Zabe

'Yan adawa da masu sa'ido daga Turai sun shiga zaben Venezuela

A karon farko tun daga shekarar 2017 jam’iyyun 'yan adawa sun shiga zaben jihohi da na kananan hukumomi a Venezuela, zaben da ya samu halartar tawagar sa ido daga Tarayyar Turai.

Al'ummar Venezuela na gudanar da zaben jihohi da na kgundumomi,21/11/21.
Al'ummar Venezuela na gudanar da zaben jihohi da na kgundumomi,21/11/21. © AP Photo/Ariana Cubillos
Talla

Kimanin ‘yan kasar Venezuela miliyan 21 daga cikin 30 ne zasu zabi ‘yan takara dubu 70 dake neman kujerun gwamnoni 23 da magadan gari 335 a ƙasar da rikicin tattalin arzikin da ba a taɓa gani ba ya shafa tare da mummunar tashin farashin kayayyaki.

Hukumar zaben kasar tace an bude rumfunan zabe tun da karfe 6 na safe agogon kasar kuma za a rufe da karfe 6 na yamma inda ake sa ran sakamako da misalin karfe 2 ko 3 na safe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.