Masu zanga-zanga kan sauyin yanayi sun sake mamaye titunan Scotland
Dubban masu zanga-zangar yanayi sun jajirce wajen yin tattaki cikin ruwan sama da iska a birnin Glasgow, domin nuna adawa da abin da suka kira gazawar tattaunawar Majalisar Dinkin Duniya kan daukar matakan da suka dace don magance dumamar yanayi.
Wallafawa ranar:
Ana sa ran gudanar makamanciyar zanga-zangar lumanar a wasu biranen kasashe da dama bayaga birnin na Glasgow, don bukatar rage amfani da man fetur da kuma taimakon gaggawa ga al'ummomin da sauyin yanayi ya shafa, musamman a kasashe masu fama da talauci.
A Glasgow, masu shirya zanga-zangar da kuma 'yan sanda sun ce kimanin mutane dubu 50,000 suka yi tattaki a titunan birnin na Scotland.
A makon da ya gabata, wani sabon rahoto da aka wallafa ya bayyana cewa, yawan fitar da iska mai gurbata muhalli zai ta’azzara a cikin wannan shekara ta 2021 zuwa matakin da aka gani gabanin bullar cutar Korona.
Rahoton wanda aka wallafa a yayin da kusan kasashen duniya 200 ke gudanar da taron sauyin yanayi a birnin Glasgow ya ce, fitar da iska mai gurbata muhalli a bana, za ta kai irin matakin da aka gani a shekara ta 2019, sabanin bara, lokacin da aka samu sassauci saboda takaita hada-hada a sanadiyar cutar Korona.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu