'Yar China ta kafa tarihin lashe kyautar Oscar
Fim din Nomadland da ke nuna yanayin rayuwar tsofaffin Amurkawa masu gararamba a cikin kwarababbiyar motar akori-kura, ya lashe lambar yabo ta Oscar saboda kyawun daukar hotonsa.
Wallafawa ranar:
Chloe Zhao wadda ta bada umarni a wasan kwaikwayon na Nomadland, ta kafa tarihin zama mace ta farko wadda ba baturiya ba da aka karrama da lambar yabo ta Oscar.
Kazalika ta zama mace ta biyu a tarihi da ta lashe kyautar a matsayinta ta mai bada umarni bayan Kathryn Bigelow wadda ta fara bude babin irin wannan tarihin a shekaarr 2010, lokacin da aka karrama ta saboda fim din “The Hurt Locker.”
Zhao ‘yar asalin China ce, amma kafafen yada labarai na kasarta ba su yada labarin nasararta ba.
A can baya, Zhao ta taba janyo cece-kuce a China saboda yadda ta caccaki kasarta a wata hira da ta yi da manema labarai.
A bangare guda, Frances McDormand ita ma ta samu lambar yabo ta gwarzuwar jaruma, yayin da Anthony Hopkins ya lashe kyautar a matsayinsa na gwarzon jarumi.
Hopkins mai shekaru 83, ya zama jarumin fina-finai mafi tsufa a tarihi da ya lashe kyautar ta Oscar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu