Isa ga babban shafi
Coronavirus

Fitattun mutanen duniya da suka kamu da coronaviru

Annobar coronavirus da ta game duniya na cigaba da rutsa wa da manyan shugabannin duniya da suka hada da Sarakuna da fitattun mawaka da ‘yan wasa da taurarin fina-finai har ma da attajirai a sassan duniya.

Firaministan Birtaniya Boris Johnson na cikin fitattun mutanen duniya da coronavirus ta kama
Firaministan Birtaniya Boris Johnson na cikin fitattun mutanen duniya da coronavirus ta kama Frank Augstein/Pool via REUTERS
Talla

A bangaren wasanni annobar murar ta COVID-19 ta kashe tsohon shugaban Kungiyar Kwallon Kafar Olympique de Marseille ta Faransa Pape Diouf mai shekaru 68, a ranar 31 ga watan Maris.

Sai kuma tsohon shugaban Kungiyar Kwallon Kafa ta Real Madrid Lorenzo Sanz da annobar ta COVID-19 ta kashe ranar 21 ga Maris, yana da shekaru 76.

A bangaren tsoffin shugabanni kuma, a ranar 30 ga watan Maris cutar ta halaka tsohon Shugaban Jamhuriyar Congo Jacques Joachim Yhombi Opango a kasar Faransa. Sai kuma Mahmud Jibril, tsohon madugun ‘yan tawayen Libya da ya jagoranci kifar da gwamnatin Mu’ammar Gaddafi, ya mutu ranar 5 ga watan Afrilu.

Wasu daga cikin fitattun shugabannin da suka kamu da cutar Coronavirus din, sun hada da Firaministan Birtaniya Boris Johnson, da Mitchel Bernier, jakadan Kungiyar Tarayyar Turai a tattaunawar Brexit.

A bangaren sarakauna kuwa, yanzu haka Yarima Charles na Birtaniya da Yariman Monaco, Albert na 2 sun kamu da wannan Cuta.

Sai kuma bangaren taurarin fina-finai, akwai Idris Elba na Birtaniya, amma dan asalin Afrika da shi ma ya kamu da ita kafin ya murmure a a ranar 31 ga watan Maris

A Afrika, ranar 9 ga Afrilu, shugaban Botswana Mokgweetsi Masisi ya sake killace kansa karo na 2, kazalika baki dayan ‘yan majalisun kasar 63 su ma sun killace kansu, bayan kamuwar likitar da aka dorawa alhakin yi musu gwaji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.