Isa ga babban shafi
Venezuela

Michelle Bachelet zata gana da Maduro a Caracas

Babbar jami’iar dake aiki da Majalisar Dinkin Duniya bangaren kare hakkokin bil adam zata kai ziyara kasar Venezuela kama daga ranar 19 zuwa 21 ga wannan watan da muke cikin sa ,inda zata yi amfani da haka tareda ganawa da Shugaban kasar Nicolas Maduro, bayan haka zata kuma tattaunawa da jagoran yan adawa Juan Gaido Shugaban majalisar kasar ta Venezuela.

Michelle Bachelet jami'ar MDD
Michelle Bachelet jami'ar MDD Reuters
Talla

Kasar ta Venezuela ce ta gayyaci Michelle Bachelet babbar jami’iar da jimawa zuwa birnin Caracasa dake babban birnin Kasar ta Venezuela.

Al’umar kasar Venezuela na fama da rashin maguguna, tattalin arzikin kasar ya durkushe, matsalloli da dama ne suka mamaye kasar tun bayan barkewar rikicin siyasa tsakanin Shugaban kasar Nicolas Maduro da Juan Gaido da ya ayyana kan sa a matsayin Shugaban kasa da kuma ke samu goyan bayan kasashe kusan 50 a Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.