Isa ga babban shafi
switzerland

Modi ya yi wa Trump shagube a taron Davos

Firaministan India Narendra Modi da ke jawabi a taron tattalin arziki da ke gudana a birnin Davos na Switzerland ya bukaci hadin kai wajen tinkarar matsalar dumamar yanayi da kuma bunkasa tattalin arziki.Tuni wasu daga cikin mahalarta taron suka fassara kalaman Modi tamkar suka ga manufar shugaba Donald Trump ta sanya Amurka akan gaba.

Firaministan India, Narendra Modi a zauren taron tattalin arziki a Davos
Firaministan India, Narendra Modi a zauren taron tattalin arziki a Davos Reuters
Talla

A karon farko kenan cikin sama da shekaru 20 da wani Firaminista daga India ke gabatar da jawabi a babban taron tattalin arziki da ake gudanarwa duk shekara a birnin Davos.

Duk da cewa Firaminista Modi bai ambaci sunan Trump ba amma ya caccaki siyasar fifita kasa akan komai.

A cewar Modi, a maimakaon mayar da hankali kan tsarin dunkulewar duniya wuri guda, siyasar fifikon kasa ce ke jan ragama.

Kalaman Modi na zuwa a yayin da ya rage kwanaki uku shugaba Trump ya gabatar da nasa jawabin a zauren taron.

A karkashin tsarin sanya Amurka akan gaba, shugaba Trump ya janye daga yarjejeniyar cinikayyar bai-daya ta arewacin kasashen Amurka, yayin da ya caccaki yarjejeniyar sauyin yanayi da kasashen duniya suka amince da ita a birnin Paris.

Kazalika Modi ya ambaci ta’addanci daga cikin manyan kalubalen da ke addabar duniya a yau.

Taron ya samu halartar shugabannin kasashen duniya da manyan jami'an bankuna da attajirai da kwararru a fannin tattalin arziki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.