Isa ga babban shafi
Libya

An ceto Bakin haure da dama a gabar Ruwan Italiya

Mahukuntan Italiya sun ce sun yi nasarar cato rayukan Daruruwan bakin haure da ke kokarin tsallakawa zuwa Turai ta kwale kwale a tekun Mediterranean

. REUTERS/Osman Orsal
Talla

Wani rahoto ya ce kimanin bakin haure 1,500 aka ceto a rana guda, cikinsu kuma akwai mata masu ciki.

Mutanen yammacin Afrika dai na bi ta Nijar ne zuwa Libya ko Algeria domin neman tsallakawa zuwa Nahiyar Turai.

Awwal Janyau ya ci karo da wani Dan Najeriya a garin Agadez da ke neman tsallakawa zuwa Turai amma rikicin da ake yi a Libya ya tursasa masa dawo wa gida.

Ya ce rayuwa a Libya akwai hatsari, mutane na mutuwa suna cikin wahala, mutane da dama na bi su tsallaka zuwa Italiya, wasunsu da daman a mutuwa, rayuwa a can akwai hatsari sosai hakan ya s azan koma gida.

To ko tun yaushe ya tsallaka zuwa libya, ya ce “Na shafe shekaru biyu a Libya ina kokarin yadda zan tsallaka Italiya domin na taba bi ta Algeria.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.