Isa ga babban shafi
Fadar Vatican

Paparoma ya bukaci masu kisa tare da cin zarafin dan adam da sunan addini su daina,

A yau lahadi albarkacin shagulgulan Ista Paparoma Francis ya yi kiran da akawo karshen zubar da jini da kuma cin zarafin bil’adama da wasu ke yi da sunan addini a kasashen Afrika da na yankin gabasta tsakkiya, har ila yau paparoman ya yabawa yarjejeniyar da aka cimma kan shirin nukliyar kasar Iran, da zama wani taki da zai kai duniya a kan tabbas

REUTERS/Alessandro Bianchi
Talla

A lokacin da ya tabo kisan gillar da aka yiwa dalibai 150 galibinsu kristoci da kungiyar Alshabab ta kasar Somaliya ta dauki alhakin kaiwa, Paparoma ya yi addu’o’I ga daukacin wadanda suka rasa rayukansu, musamman matasan da harin na jami’a’ar Garissa ta kasar Kenya ya rutsa da su,

Har ilayau shugaban addinin Cristan na duniya ya yi fatan samun kwanciyar hankali a kasashe irinsu Nigeria,Sudan ta kudu Libiya da daukacin yankunan Sudan da JDC
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.