Isa ga babban shafi
Italiya-Libya

Italiya za ta jagoranci yaki da Mayakan Libya

Gwamnatin italiya ta ce a shirye ta ke domin jagorantar gamayyar kasashen duniya, don yakar mayakan jihadi a Libya. Sanarwa na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke kwashe mutanenta da ke kasar mai fama da rikici.

Mayakan da ke da'awar Jihadi a kasar Libya
Mayakan da ke da'awar Jihadi a kasar Libya AFP PHOTO/MAHMUD TURKIA
Talla

Ministan tsaron Italiya Roberta Pinotti ya ce a shirye suke domin jagorantar gamayyar dakaru kasashen yammaci da Amurka wajen yaki da mayakan da ke da’awar jihadi a Libya.

Pinotti ya ce sun dauki tsawon watanni suna tattaunawa akan yadda za su bayar da gudumawar tunkarar matsalar ‘Yan ta’adda a Libya.

A ranar Juma’a Italiya ta gargadi ‘yan kasarta akan su yi taka-tsantsan wajen tafiya Libya bayan ta yi amfani da jirgin ruwa wajen debo akalla ‘yan kasar 100 don komar da su gida.

Rikicin Libya dai a kullum na ci gaba da daukar sabon fasali tun bayan kawar da gwamnatin Marigayi Kanal Gaddafi a 2011.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.