Canada-Ukraine
Canada ta sanya wa wasu 'yan kasashen Rasha da Ukraine takunkumi
Kasar Canada ta sanya wa wasu jami’an gwamnatin kasashen Rasha da Ukraine su 11 takunkimin tattalin arziki, tare da haramta musu shiga kasar. Hukumomin kasar sun ce sun dauki wannan matakin ne sakamakon rawar da suka taka, wajen take ‘yancin kasar ta Ukraine.Wannan matakin na zuwa ne a daidai lokacin da yunkurin da ake yi, na samar da zaman lafiya a kasar ke halin rashin tabbas, kuma shugaban Rasha Vladmir Putin ya umarci sojan kasar su ci gaba da zama cikin shirin yaki.Takunkumin ya biyo bayan wadanda Amurka da kungiyar tairayyar Turai suka kakabawa kasashen 2.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar: