Isa ga babban shafi
Amurka-Iran-Isra'ila

Isra'ila ta ki amincewa da yarjejeniyar Iran da kasashen yammacin duniya

Firaministan Israila Benjamin Netanyahu ya bayyana yarjejeniyar da kasashen yammacin duniya suka kulla da Iran kan shirin nukiliyar kasar a matsayin kuskure.Yayin da yake mayar da martani kan amincerwa da yarjejeniyar, Netanyahu yace ba zasu taba barin kasar da taki amincewa da wanzuwar Israila ta samu makamin da zata cimma biyan bukatar haka ba.Fira Ministan yace idan kawayen Israila sun yi kuskure, hakkin sa ne yayi furuci akai.A halin da ake ciki kuma, kasar ta Isra’ila ta amince da gina sabbin gidajen Yahudawa, 829 a yammacin kogin Jordan.Wata kungiyar kare hakkin dan Adam mai suna Peace Now ta tabbatar da hakan, inda mai magana da yawun kungiyar Lior Amihai, yace majalisar sojan da ke aiki a yankin yammacin na kogin na Jorada ne suka amince da matakin.Masu lura da lamura na ganin wannan a matsayin wani mataki na nuna bacin ranta da yarjejeniyar nukiliyar da kasashen Yammacin duniya suka kulla da Iran. Shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas ya yi gargadin cewa gine ginen da Isra’ila ke yi a yankunan Palasdinawa na barazana ga shirin zaman lafiya a yankin na gabas ta tsakiya.Falasdinawa sun sanya dakatar da gine gine a Yankunan su, a matsayin yarjejeniyar tattaunawa da kuma amincewa da duk wani shirin zaman lafiya da Israila.  

Firaministan kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu
Firaministan kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu REUTERS/Debbie Hill/Pool
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.