Columbia
An fara samun baraka tsakanin Gwamnatin Columbia da ‘Yan tawaye
Gwamnatin Kasar Colombia tace yunkurin hallaka tsohon shugaban kasar, Alvaro Uribe, da ‘Yan Tawayen FACR ke yi, na iya dakushe tattaunawar zaman lafiyar da ake yi a kasar Cuba. Tsohon mataimakin shugaban kasar, Humberto de la Calle, wanda ke cikin wakilan da ke tattaunawa da ‘Yan Tawayen, yace ba za su taba amincewa da irin wanna yunkuri ba.
Wallafawa ranar:
Talla
La Calle yace, ana tattaunawa ne don kauda duk wata barazana, amma kuma idan ana samun haka, to shirin zaman lafiyar ba zai kai ga nasara ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu