Isa ga babban shafi
UN-Korea

Ban Ki-moon ya sake rokon Koriya ta Arewa ta sassauta barazanarta

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, ya sake rokon kasar Koriya ta Arewa ta dai na daukar matakan da ke harzuka kasashen duniya, sakamakon wani rahoto da ke nuna cewar za ta sake gwajin makamin nukiliya.

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya rike karamar Bindiga tare da dakarun shi na (KPA), a wani Hoto da aka dauka daga Telebijin
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya rike karamar Bindiga tare da dakarun shi na (KPA), a wani Hoto da aka dauka daga Telebijin Reuters
Talla

Ban ya yi wannan gargadi ne a birnin Hague, inda ya ke cewa, kasar Koriya ta Arewa ba za ta ci gaba da kalubalantar Majalisar Dinkin Duniya da kuma kasashen duniya ba.

Sakataren ya ce, wannan kira da ya yi, sako ne da ga kasashen duniya, don ganin Kasar ta Koriya ta Arewa ta kawo karshen tankiyar da ake samu, da kuma kaucewa gwajin makaman nukiliya.

Wannan kuma na zuwa ne bayan Kasar Koriya ta kudu, ta yi zargin cewar, akwai alamun Koriya ta Arewa na shirin gwajin makamin, wanda kasar Amurka tace ba za ta yi mamaki ba, idan haka ta faru.

Kasar Japan ta umurci sojojinta da su harbo duk wani makamin Koriya ta Arewa da aka harba kan kasar, yayin da China ta bayyana rashin goyan bayanta da shirin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.