Isa ga babban shafi

Akwai Alamun Cim ma yarjejeniyar tsagaita Wuta tsakanin Hamas da Isra’ila

Adadin wadanda suka mutu sun haura 100 a hare haren da Isra’ila ke kai wa a Zirin Gaza yayin da Hamas ke ci gaba da harba Rokoki a Kudancin Isra’ila. Rahotanni sun ce shugabannin Isra’ila sun kwashe lokaci suna tattaunawa domin amincewa da yarjejeniyar Masar ta tsagaita wuta kafin ziyarar Wakilan shugabannin kasashen Larabawa da wakilan Majalisar Dinkin Duniya a birnin Kudus.

Hare haren da Isra'ila ta kai sun kashe fararen hula tare da raunata mutane da dama
Hare haren da Isra'ila ta kai sun kashe fararen hula tare da raunata mutane da dama REUTERS/Suhaib Salem
Talla

A Zauren Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, kasar Amurka tace za ta kalubalanci duk wani kudiri da zai sabawa tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu.

Amma kasar Kasar Rasha ta zargi Amurka da hawa kujerar na-ki, kan shirin kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, na yin Allah waddai da harin fin karfin da Isra’ila ke yi wa Falasdinawa a Yankin Gaza.

Jakadan Rasha a kwamitin Sulhu, Vitaly Churkin, yace za su bukaci babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya dauki mataki akai, idan hakan ya gagari kwamitin Sulhu.

Rahotanni daga Isra’ila sun ce Benjamin Netenyahu tare da manyan Jami’an gwamnatin kasar guda Tara sun kwashe lokaci mai tsawo suna tattaunawa domin nazarin tsagaita wuta ko akasin haka.

Yanzu haka an shiga kwanaki Bakwai Isra’ila na ruwan wuta ta sama a Gaza tun harin farko da ya kashe babban kwamandan Hamas Ahmad Jabbari. Yayin da kuma Hamas ke kai hare haren Rokoki a yankunan Yahudawa.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya kai ziyara Birnin Al Kahira domin tattauna hanyoyin tsagaita wuta, amma Shugaban Hamas Khaleed Meshal yace za su amince da matakin tsagaita wuta idan Isra’ila ta janye takunkuminta a Gaza tsawon shekaru Shida.

Jekadiyar Amurka a zauren Majalisar Dinkin Duniya Susan Rice tace sai bangarorin biyu sun dauki matakin tsagaita wuta ne za’a samu maslaha.

Kasashen Amurka da Jamus da Birtaniya da Faransa dukkaninsu sun bayyana damuwa ga kalaman kungiyar kasashen Larabawa saboda rashin bayyana hare haren rokokin da Hamas ke kai wa a yankunan Isra’ila.

Amma daruruwan mutanen Gaza ne suka kauracewa gidajensu saboda luguden wuta da Isra’ila ke yi.

Rahotanni sun ce mutane sama da 115 suka mutu a Gaza a hare hare 1,350 da Isra’ila ta kai, Amma Sojin Isra’ila sun ce Rokoki 640 ne aka harba zuwa yankin Kudancin kasar.

Wannan rikicin na zuwa ne kafin gudanar da zabe a kasar Isra’ila a ranar 22 ga watan Janairu inda Hamas ke zargin Natenyahu ya kaddamar da yaki ne domin samun farin jinin Yahudawa a yakin neman zaben shi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.