Isa ga babban shafi
Amurka

Bill Clinton ya yi kira ga Amurkawa da su zabi Obama

Tsohon shugaban kasar Amurka Bill Clinton, ya yi kira ga Amurkawa, da su zabi Barack Obama karkashin jam’iyyar Demokrat bayan ya bayyana goyon bayan shi ga shugaban a yakin neman zaben Jam’iyyarsu.Clinton ya kuma kara da yin gargadin cewa jam’iyar Republican za ta jefa tattalin arzikin kasar cikin halin ni-‘yasu idan hart a kafa gwamnati.  

Tsohon shugaban kasar Amurka, Bill Cinton
Tsohon shugaban kasar Amurka, Bill Cinton AFP Photo/Paul J. Richards
Talla

A cewarsa, zaben Obama shi ne mafita ga tattalin arzikin Amurka, domin daidaita tattalin arzikin kasar da ya samu nakasu daga Gwamnatin George W. Bush da Obama ya gada.

Tsohon shugaban kasar ta Amurka, shi ne shugaba na farko da ya yi tazarce karkashin jam’iyyar Demokrat tun yakin duniya na biyu, shi kuma ne ya zabi Obama a matsayin dan takara.

Taron na ‘Yan Demokrat, ya fara ne da wani bayani da Uwar gida, Michelle Obama ta yi a ranar Talata, a yayin da magoya bayan na Obama ke ta duruwa zuwa garin.

Clinton dai ya kasance har yanzu yana da farin jinni a wurin Amurkawa kamar a lokacin da aka rantsar da gwamnatinsa ashekarar 1993 inda a wani binciken jin ra’ayin Amurkawa da gidan telebijin na CNN ya gudanar, ya samu kashi 66.

A kuma cikin jawabinsa, Clinton ya kara fadawa Amurkawa dalilin da ya sa ba a so su zabi ‘Yan Republicans, inda ya yi zargin cewa, gwamnatin George W. Bush, wacce ta bar kan mulki shekaru hudu da su ka wuce, ta bar tattalin arzikin kasar cikin halin ni ‘yasu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.