Isa ga babban shafi
Amurka-Pakistan

Dakarun Amurka sun kashe Al Libi Kwamandan Al Qaeda

Jami’an tsaron Amurka sun ce sun kashe wani bababn jami’in kungiyar Al Qaeda, Abu Yahya al-Libi, a wani harin da da kakarun kasar suka kai da jirgin sama mai sarrafa kansa a Pakistan. FadarWhite House tace kashe Libi, babbar koma baya ce ga kungiyar Al Qaeda, saboda rawar da yake takawa wajen shirya kai hare hare.

Abu Yahya al-Libi babban kwamandan kungiyar Al Qaeda
Abu Yahya al-Libi babban kwamandan kungiyar Al Qaeda
Talla

Abu Yahya al Libi dan asalin kasar Libya ne kuma mataimakin shugaban Al Qaeda.

Abu Yahya al-Libi ana danganta shi a matsayin mutum mai tsatstsauran ra’ayi wanda ya tsere daga Gidan yarin Amurka a Afghanistan.

A ranar litinin ne dakarun Amurka suka kashe Al Libi a kauyen Khassu Khel arewacin Waziristan. An smau mutuwar mutane Takwas a harin na Amurka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.