Amurka - Korea ta kudu
Amurka, Korea ta kudu sun fara atisayen soji
KASASHEN Amurka da Korea ta kudu, sun kaddamar da wani atisayen soji, dauke da dubban sojoji, dan magance duk wata barazana daga Korea ta Arewa.Atisayen da za’a kwashe kwanaki goma anayi, shine irinsa na farko, bayan nitsar da jirgin ruwan yakin Korea ta kudu, a watan Maris da ya gabata.Shugaba Lee Myung Bak, wanda yayi kiran hadewar Korea ta kudu da Korea ta Arewa a karshen mako, yace atusayen shirin zaman lafiya ne, da kuma yaki.
Wallafawa ranar: