Isa ga babban shafi

Amurka na zargin 'yan Najeriya 18 da amfani da lasisin aikin jinya na bogi

Kasar Amurka ta gurfanar da akalla ma’aikatan jinya 18 ‘yan Najeriya a gaban kotu bisa zarginsu da karbar takardun shaidar karat una bogi.

Wasu ma'aikatan jinya a Najeriya.
Wasu ma'aikatan jinya a Najeriya. © Twitter/ NANNM
Talla

Kwalejin horas da aikin jinya ta Texas ta tuhumi ma’aikatan lafiya a Kotun Lardin Kudancin Florida da ke cewa ma’aikatan jinya sun shiga cikin wani shirin zamba wanda ke bada lasisin aikin jinya na bogi.

Dangane da daftarin tuhumar da aka shigar gaban kotun, tsarin ya nuna yadda ake sayar da takardun shaidar nazarin aikin jinya na bogi da aka samu a wata kwalejin horaswa da ke Florida,  ga mutanen da ke neman lasisi da ayyuka a matsayin ma’aikatan jinya.

Siyan takardar shaidar aikin jinya ga wadanda ba su cancanta ba, laifi ne da ke iya yin barazana ga lafiya da kuma cin zarafi ga aikin jinya, in ji Omar Aybar, wakili na musamman da ke bincike kan zargin.

‘Yan Najeriyar da ake tuhumar sun hada da: Abiodun Felicia; Adelakun Aveez; Adelekan Adewale; Adeoye Temitope; Adewale Abidemi; Afolabi Toun; Afolabi Omowunmi; Agbo Steve; da Ajibade Omotayo.

Sauran su ne; Akande Olabisi; Akhigbe Catherine; Akinrolabu Folasade; Ako Esiri; Akpan Rosemary; Alimi Bukola; Ani Ndirika; Aroh Nchekwube; da Ayodeji Sherifat.

Idan an same su da laifin, kowanen su fuskanci zaman gidan yari na tsawon shekaru 20, kamar yadda takardun kotu suka bayyana a ranar 25 ga watan Janairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.