Isa ga babban shafi

Likitoci sun shiga kwana na bakwai da fara yajin aiki a Kenya

Likitoci a Kenya sun shiga kwanaki na bakwai a yajin aikin gama gari da suka fara a fadin kasar, bisa zargin gwamnati da gaza aiwatar da wasu alkawuran da ta dauka na yarjejeniyar da aka rattabawa hannu a shekarar 2017 bayan yajin aikin kwanaki 100 da ya yi sanadiyar mutuwar mutane a asibitoci.

Yadda 'yan sanda ke kokarin dakatar da masu zanga-zanga, yayn da likitocin kasar ke neman a cika alkawarin da aka daukar musu a shekarar 2013.
Yadda 'yan sanda ke kokarin dakatar da masu zanga-zanga, yayn da likitocin kasar ke neman a cika alkawarin da aka daukar musu a shekarar 2013. REUTERS/Thomas Mukoya
Talla

Kungiyar likitocin kasar Kenya da kungiyar likitocin hakora sun ce sun shiga yajin aikin ne domin sha’anin walwalarsu da kuma gazawar gwamnati wajen daukar kwararrun likitoci 1,200 aiki.

Shugabannin kungiyar sun ce likitoci 4,000 ne ke yajin aikin duk da umarnin da kotun ma’aikata ta bayar na dakatar da yajin aikin domin samun damar tattaunawa da gwamnati.

Amma likitocin sun ce sun yi watsi da umarnin kotun kamar yadda gwamnati ta yi watsi da umarnin kotu har sau uku game da karin albashin ma’aikatan lafiya tare da maido da likitocin da aka dakatar aiki.

A shekarar 2017, likitoci a asibitocin gwamnati Kenya suka gudanar da yajin aikin kwanaki 100 mafi dadewa da aka taba gudanarwa a kasar domin neman karin albashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.