Gbagbo ya bayyana aniyarsa ta sake neman shugabancin Cote d'Ivoire
Tsohon shugaban kasar Ivory Coast, Laurent Gbagbo ya amince ya yi wa jam'iyyarsa takaran neman shugaban kasa a zaben 2025.
Wallafawa ranar:
Katinan Kone, kakakin jam'iyyar African People's Party - Cote d'Ivoire wanda Gbagbo ya kafa a shekarar 2021 ne ya sanar da matakin bayan wani taro da kwamitin koli na jam'iyyar ya gudanar a ranar Asabar.
A shearer 2021 ne Gbagbo ya kuma gida bayan da Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) ta wanke shi daga zargin hannu a yakin basasar kasar na shekarar 2019 sakamakon kin amincewa da shan kaye a zaben 2010.
Jam'iyyarsa ta farko
Ya rasa iko da jam'iyyar da ya kafa a baya, wato Ivory Coast Popular Front (IPF), yayin da yake zaman kurkuku yana jiran shari'a a Netherlands tsawon shekaru da dama, amma har yanzu yana riƙe da manyan magoya bayansa da ya amince a gida.
Ana sa ran gudanar da zaben kasar da ke yammacin Afirka a watan Oktoba na shekarar 2025. Shugaba Alassane Ouattara, mai shekaru 82, wanda aka sake zaba a shekara ta 2020 bai bayyana ko zai sake tsayawa takara ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu