Kasashen Afirka na taro kan yadda za a kawar da cutar Malaria daga nahiya
Ministocin lafiya daga kasashen Africa 12 da suka fi fama da matsalar cutar zazzabin cizon sauro sun yi wata ganawa ta musamman a birnin Yaounde na kasar Kamaru.
Wallafawa ranar:
Taron nasu na da nufin gano hanyoyin da za’a bi wajen magance illolin cutar da kuma yadda za’a yi amfani da hanyoyi na zamani don kawo karshenta.
Da yake jawabi, ministan lafiyar kasar Mali, Assa Badiallo ya ce babu wata kasa da zata iya magance matsalar cutar la’akari da tasirin ta, amma da hadin kai, cutar ka iya zama tarihi cikin dan kankanin lokaci.
Kaso 70 cikin 100 na mace-macen da ake samu dalilin cutar malária na faruwa ne a kasashen Africa musamman Burkina Faso, Cameroon, Jamhuriyar dimokradiyyar Congo, Ghana, Mali, Mozambique, Niger, Nigeria, Sudan, Uganda da Tanzania.
Kididdiga ta nuna cewa cutar na kashe mutane akalla dubu daru 6 kowacce shekara a Nahiyar Africa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu