Isa ga babban shafi

Jiragen sama biyu sun yi taho mu gama a kasar Kenya

Bayanai daga kasar Kenya, na cewa wasu jirage biyu sun yi taho mu gama da juna yayin da suka rikito a tsakiyar wajen shakatawa na Nairobi National Park lamarin da yayi ajalin mutane 2.

Hatsarin ya yi sanadin rayukan mutum biyu
Hatsarin ya yi sanadin rayukan mutum biyu © AFP
Talla

Dukannin jiragen biyu sun tashi ne daga filin jirgin Wilson Airport, kuma ba da jimawa ba suka yi karo da juna inda suka fadi.

Tuni kamfanonin jiragen biyu suka tabbatar da faruwar lamarin a hukumance.

Kawo yanzu dai kamfanonin jiragen biyu sun sanar da fara binciken kan musabbabin hadarin jiragen.

Mutum 44 ne hukumomi suka tabbatar sun jikkata sakamakon aukuwar lamarin a halin yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.