Isa ga babban shafi

An samu koma bayan yaki da annobar kwalara a Afirka - MSF

Kungiyar likitoci ta duniya, ta ce an samu koma baya a bangaren yaki da annobar amai da gudawa ko kuma kwalara a Afirka, sakamakon raguwar tallafin da ake samu na alluran rigakafi.

Yadda mutane ke karbar kulawar gaggawa a wata cibiyar lafiya da aka samar a filin wasa na Lusaka da ke kasar Zambia, ranar 18 ga Janairu, 2024.
Yadda mutane ke karbar kulawar gaggawa a wata cibiyar lafiya da aka samar a filin wasa na Lusaka da ke kasar Zambia, ranar 18 ga Janairu, 2024. © Namukolo Siyumbwa / Reuters
Talla

Karancin allurar rigakafin ya zo ne a daidai lokacin da kudancin Afirka ke fama da barkewar cutar kwalara wadda ta kashe mutane 700 a Zambia kadai.

Kungiyar likitoci ta Doctors Without Borders ta ce karancin ya shafi kungiyoyin ta da ke kokarin yakar annobar a kasashe sama da 16.

Masana kiwon lafiya sun bukaci kamfanoni da su hanzarta samar da allurar.

A watan Janairu, kasar Zambia ta kaddamar da wani shirin wayar da kai da UNICEF ke marawa baya don yi wa mutane miliyan 1.5 allurar rigakafin cutar kwalara.

Barkewar cutar da aka samu a 2023 a yanzu ta yadu zuwa dukkanin yankunan kasar, lamarin da ya tilastawa hukumomi mayar da filayen wasanni cibiyoyin kula da lafiya tare da jinkirta bude makarantu.

A cewar kungiyar Save the Children, an samu karuwar cutar kwalara a kasashen Malawi, Zimbabwe, da Mozambique daga shekarar 2022 zuwa 2023.

Adadin kamuwa da cutar ya karu daga 26, 250 zuwa sama da 95 300, inda sama da mutum 1 600 suka mutu a cikin kasashe uku kacal, wanda ya sa ya zama mafi munin annobar kwalara a cikin shekarun da suka gabata da aka taba samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.