Isa ga babban shafi

Najeriya ta koma baiwa Nijar lantarki bayan cirewa kasar takunkumai

Gwamnatin Najeriya ta amince da mayarwa jamhuriyar Nijar wutar lantarki, matakin da ke biyo bayan janyewa kasar takunkumai da kungiyar ECOWAS ta yi a jiya Asabar.

Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu AFP - KOLA SULAIMON
Talla

A  watan Agustan bara ne dai gwamnatin Najeriya ta yanke shawarar kaste wutar lantarki da ta ke baiwa jamhuriyar Nijar, a wani bangare na hukunta sojojin da suka hambarar da gwamnatin shugaba Bazoum.

Katse wutar lantarkin ya jefa jama’ar kasar cikin mawuyacin hali, tare da durkusar da tattalin arzikin da kassara masu kananan sana’o’i.

Bayan sanar da mayar da wutar lantarkin, gwamnatin ta Najeriya bukaci sojojin na Nijar su bada hadin kan da ya kamata wajen mayar da kasar karkashin gwamnatin farar hula.

Ko da yake jawabi, shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu wanda kuma shine shugaban ECOWAS ya ce akwai bukatar jama’ar Nijar su fahimci cewa ba wai an katsewa kasar wutar lantarki bane don kawai a jefa su cikin matsala ba, an yi haka ne don tilastawa sojojin hawa kan teburin sulhu.

Ya ce a yanzu ECOWAS zata sauya salo ta hanyar amfani da diplomasiyya wajen tabbatar da mulkin dimokradiyya a jamhuriyar Nijar da sauran kasashen da ke hannun sojoji a Africa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.