Shugaban Senegal ya yi alkawarin gudanar da zabe da wuri-wuri
Shugaban kasar Senegal Macky Sall, wanda ke fuskantar matsananciyar matsin lamba a cikin gida da wajen kasar, ya sha alwashin shirya zaben shugaban kasa da wuri-wuri, bayan da da majalisar tsarin mulkin kasar ta yi watsi da matakin da ya dauka na jinkirta zaben na wannan wata.
Wallafawa ranar:
Yunkurin da Shugaban na Senegal ya yi na dage zaben ranar 25 ga watan Fabrairu har zuwa Disamba ya janyo rikici cikin kasar ta Senegal mafi muni cikin shekaru da dama.
Matakin dai ya haifar da cece-kuce da zanga-zangar da ta yi sanadiyar mutuwar mutane.
Hukuncin da majalisar tsarin mulkin kasar ta yanke ranar Alhamis na soke jinkirin zaben ya jefa kasar cikin rashin tabbas.
Shugaban kasar ya kuduri aniyar aiwatar da cikakken hukuncin majalisar tsarin mulkin kasar,” in ji fadar shugaban kasar a cikin wata sanarwa.
"Don haka, ba tare da bata lokaci ba, shugaban kasar zai gudanar da shawarwarin da suka dace don shirya zaben shugaban kasa da wuri-wuri."
Macky Sall, wanda ke kan karagar mulki tun a shekarar 2012, ya ce ya dakatar da zaben da za a yi a wannan watan ne saboda takaddamar da ake yi game da soke zaben da ake yi da ‘yan takara da kuma nuna damuwa kan komawar tarzoma da ake gani a 2021 da 2023.
Daga baya majalisar ta amince da jinkirin zuwa ranar 15 ga watan Disamba, amma sai bayan da jami’an tsaro suka shiga ginin tare da cire wasu ‘yan adawa a cikin majalisar.
Kuri'ar ta share fagen wa'adin Sall -- wanda wa'adinsa na biyu zai kare a watan Afrilu,ya ci gaba da zama kan karagar mulki har sai an girka magajinsa.
An kashe mutane uku a yayin zanga-zangar nuna adawa da jinkirin kada kuri’a, inda jami’an tsaro suka dakile yunkurin gangamin.
Mutane kalilan ne suka amsa kiran zanga-zangar da aka yi a Dakar babban birnin kasar a jiya.
'Yan adawar dai sun yi Allah wadai da matakin na Shugaba Sall a matsayin wani juyin mulki na kundin tsarin mulkin kasar, inda suka ce jam'iyyarsa na fargabar shan kaye a akwatin zabe na dan takararta, Firayiminista Amadou Ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu