Isa ga babban shafi

Rahoton jana'izar Mahamane Salisssou Hamissou na RFI Hausa a garin Tsibiri

Yau da safe ne aka gudanar da jana'izar Mahaman Salissou Hamissou, abokin aikin mu na Sashen Hausa na RFI da Allah ya yiwa rasuwa daren laraba sakamakon hadarin mota a Katsina dake Najeriya. An dai gudanar da jana'izar ce a Tsibiri dake Maradin Jamhuriyar Nijar.

Salissou Hamissou, journaliste à la rédaction de RFI en haoussa, décédé le 14 février 2024, à la suite d’un accident de la route au nord du Nigeria.
Salissou Hamissou, journaliste à la rédaction de RFI en haoussa, décédé le 14 février 2024, à la suite d’un accident de la route au nord du Nigeria. © RFI
Talla

 

An haife shi ne a ranar 31 ga watan Agustan shekarar 1972 a birnin Yamai da ke Jamhuriyar Nijar kuma ya yi karatun addini da na boko a birnin.

Ya shafe sama da shekaru 30 yana aikin jarida, inda ya yi aiki da wasu kafafen yada labarai na cikin gida a Nijar kamar Amfani da R&M da kuma Tambara, gabanin tafiya sashen Hausa na Radio Iran.

Shi ne mutun na farko da ya fara karanta labaran duniya a sashen Hausa na RFI shekaru 17 da suka gabata, inda a wancan lokacin ya jagoranci labaran karfe 5 na yamma agogon Najeriya da Nijar.

Latsa alamar sauti don sauraron rahoton Salissou Issa daga Maradi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.