Isa ga babban shafi

Gwamnatin Sojin Nijar ta soke manhajar Yamaro mai wayar da kan mata

Ministan sadarwa na Nijar a jiya Laraba ya ba da umarnin cire manhajar Yamaro da wata kungiya mai zaman kanta ta kirkiro da nufin wayar da kan mata game da lafiyar, jima'i da haihuwa.

Wasu 'yan mata tsaye cikin gonar gero a kauyen Hawkantaki dake Jamhuriyar Nijar.
Wasu 'yan mata tsaye cikin gonar gero a kauyen Hawkantaki dake Jamhuriyar Nijar. AP - Jerome Delay
Talla

Ministan Sadarwa,da Tattalin Arziki na bangaren da ya shafi fasao’i na zamani Sidi Mohamed Raliou ya gana da mambobi biyu na kungiyar mai suna NGO Women muhalli da suka hada da Mijinguiné Abdou Maman Sani "da shugaban sadarwa, Salac Moumouni Aichatou" a wanan haduwa ne Ministan ya sanar da su bukatar hukumomin kasar ta Nijar da cewa ya zama tilas kungiyar ta cire wannan manhaja da shafin intanet,manhaja da ta shafi wayar da kan mata game da lafiya,jima'i da haihuwa a kasar ta Nijar,da kuma mata za su iya gudanar da bincke daga wayoyin sadarwa.

Mata  a wani i asibitin garin Agadez
Mata a wani i asibitin garin Agadez © ISSOUF SANOGO / AFP

Ministan ya bayyana cewa ,bukatar ta shafi duk wasu hanyoyin sadarwa da wannan kungiya ke amfani da su.

Kungiyar WEP Niger mai zaman kan ta reshe ne na kungiya da aka samar da ita a Najeriya.

Yan lokuta da sanar da matsayin hukumomin na Nijar,kungiyar  ba ta fitar da sanarwa ba.

Dalibai a makaranta a kasar ta Nijar
Dalibai a makaranta a kasar ta Nijar AFP - BOUREIMA HAMA

A farkon watan Fabrairu ne kungiyar ta sanar da kaddamar da aikace-aikacen Yamaro a kasar ta Nijar inda al'ummar kasar kusan kashi 95 cikin dari musulmai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.