Isa ga babban shafi

An bude taron kungiyar IGAD a Uganda da zai mayar da hankali kan rikicin Sudan

Rikicin Sudan, da kuma takun saka tsakanin Somalia da Masar ne batutuwan da zasu mamaye taron kungiyar kasashen gabashin Africa da aka bude jiya Alhamis.

Wasu daga cikin shugabannin da suka halarci taron
Wasu daga cikin shugabannin da suka halarci taron © state house Kenya
Talla

Bayanai na cewa shugabannin Sudan ta kudu, Kenya, Djibouti da kuma Somalia sun hallara a Uganda mai masaukin baki.

 

Wannan dai shine taron da shugaban mulkin sojin Sudan Abdulfattah Al-Burhan ya yi fatali da gayyata, bayan da gwamnatin sa ta sami labarin masu shirya taron sun gayyaci shugaban RSF Hamdane Daglo, wanda shine ake tafka yaki a kasar.

 

Tun bayan fara yakin na watan Afrilun bara, janar din sojin biyu basu gamu fuska da fuska ba.

 

Wannan dai na kara nuna yadda shugaban sojin Al-Burhan ke ci gaba da rasa tasiri, la’akari da yadda shugabannin kasashen gabashin African suka marabci Daglo a ziyarar da ya kai wa kasashen a dai-daikun su watan jiya.

 

Bayanai sun tabbatar da yadda RSF ke ci gaba da samun nasara kan sojojin kasar, tare da kwace iko da wasu sassa masu muhimmanci, duk kuwa da amincewa da zama kan teburin sulhu da Daglo din yayi da shugaba Burhan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.