Isa ga babban shafi

Malamin cocin da yayi sanadin mutuwar mabiyansa 400 a Kenya ya gurfana gaban kotu

Mahukuntan kasar Kenya sun shirya gurfanar da shugaban wata gagarumar kungiyar asiri kuma limamin Coci Paul Makhenzie gaban kotu bisa zargin kisan kai da kuma ta’addanci.

Paul Mackenzie wanda ake zargi da kisan jama'ar
Paul Mackenzie wanda ake zargi da kisan jama'ar REUTERS - STRINGER
Talla

Mackhenzie ya shiga hannun jami’an tsaro ne bayan da ya umarci mabiya cocinsa, da su daina cin abinci har su mutu don samun tsira da kuma saduwa da Yesu.

 

Tun bayan kama shi a watan Afrilu, Mackenzie ya musanta dukannin zarge-zargen da ake yi masa a gaban ‘yan sanda, sai dai kuma ba’a kai shi kotu ba har sai da mahukunta shari’a suka bada wa’adin makonni biyu na ko dai a sake shi ko kuma a gurfanar da shi a gaban kotu.

 

Mabiyan sa sama da 400 ne suka mutu cikin daji a sakamakon biyayya ga umarnin nasa.

 

Wannan na cikin aikin tsafi da ya lakume rayukan mutane mafi yawa a duniya, kuma tuni tawagar masu shigar da kara suka rubute jerin tuhume-tuhume har 95, da suka hadar da kisan dan adam, ta’addanci da kuma azabtarwa.

 

Amma a nasa bangaren lauyan Mackenzie, ya ce wanda yake karewa bai aikata mafi yawa daga cikin laifukan da ake tuhumar sa ba, sai dai yana baiwa jami’an tsaro hadin kan da ya kamata yayi binciken su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.