Isa ga babban shafi

Hukumar lafiya ta duniya zata aikewa da Zambia allurar rigakafi amai da gudawa

Hukumar Lafiya ta duniya ta shirya aikewa da kasar Zambia kashin farko na allurar rigakafin cutar amai da gudawa, dai-dai lokacin da annobar ke kara kamari a kasar.

Hedikwatar hukumar lafiya ta duniya a birnin Geneva da ke kasar  Switzerland.
Hedikwatar hukumar lafiya ta duniya a birnin Geneva da ke kasar Switzerland. REUTERS - Denis Balibouse
Talla

Bayanai sun ce WHO zata aike da rigakafin cutar sama da guda dubu 500.

Kasar da ke kudancin Africa ta shafe watanni uku tana fama da barkewar annobar, dalilin da ya tilasta ci gaba da rufe makarantu a bana.

Kawo yanzu cutar ta kashe sama da mutane 374, cikin su guda 12 cikin sa’o’i 24 da suka gabata, a yayin da sama da 9,580 ke kwance a asibitoci yanzu haka, sanadin cutar da ke da karfin kashe dan adam cikin sa’o’I kalilan.

WHO din ta yi hadin gwiwa ne da kamfanin samar da alluran rigakafi na Gavo global alliance wajen samar da wadannan allurai, da zummar taikamawa mahukunta don kawo karshen ta.

A jawabin da minister lafiya ta kasar Sylvia Masebo ta yi, ta yaba da shirin na hukumar lafiya, inda ta ce karancin rigakafin cutar shi ne babban dalilin yaduwar ta.

Ta ce kawo yanzu kasar ta karbi allura sama da miliyan 1 da dubu 400 cikin guda miliyan 1 da dubu 700 da WHO din ta amince a bata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.