Isa ga babban shafi

An fara samun raguwar masu harbuwa da cutar HIV a Afirka ta Kudu

Karon farko an samu raguwar adadin masu fama da cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV a Afirka ta Kudu, amma hukumomin kasar sun ce za a ci gaba da yin taka tsantsan domin dakile yaduwar cutar.

Afirka ta Kudu dai ita ce kan gaba na maasu fama da ccutar HIV a duniya.
Afirka ta Kudu dai ita ce kan gaba na maasu fama da ccutar HIV a duniya. © CSIS
Talla

Kasar dai ta kasance kan gaba cikin jerin kasashen da ke fama da ccutar HIV a duniya, shekaru 40 da suka gabata, abin da ya yi sanadin rayukan miliyoyin mutane.

Cibiyar nazarin kwayoyin cutuka ta Afirka ta kudu, ta ce binciken da aka gudanar ya gano cewa daga cikin mutum miliyan 62, kusamn miliyan takwas ne ke fama da wannan cuta ta sida a kasar.

Rahoton ya ci gaba da cewa an samu raguwar kaaso 14 na adadin masu dauke da wannan cuta, idan aka kwatanta da rahoton da aka tattara a shekarar 2017.

Khangelani Zuma, shugaban cibiyar nazarin cutuka, kuma jagoran tawagar binciken, har yanzu ba a gano abin da ya kawo raguwar adadin masu kamuwa da wannan cut aba..

Sai dai ya lura da cewa, bullar annobar Coronavirus, wadda ta kasance babbar barazana, ta taimaka wajen kawo raguwar wannan cuta a tsakanin mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.