Isa ga babban shafi

Jagoran 'yan adawan Senegal ya fara yajin cin abinci

Hukuncin shekaru 2 da kotun ta yankewa Sonko a ranar 1 ga watan Yulin da ya gabata ya tayar da tarzoma wadda ta yi sanaddin mutuwar mutane fiye da 20, wanda tuni gamnatin kasar ta alakanta wannan da dan adawa Sonko. 

Jagoran 'yan adawan Senegal Ousmane Sonko.
Jagoran 'yan adawan Senegal Ousmane Sonko. © Facebook SonkoOfficiel
Talla

Tun farko mai gabatar da kara na gwamnatin kasar, ne ya sanar da karin wasu zarge-zarge 7 da ake tuhumar Mista Sonko da suka hadar da tayar da tarzoma a kasar. 

A wani sako da ya wallafa a shafin sa na sada zumunta, Mr. Sonko ya ce yayin da ake ci gaba da fuskantar tsanani, matsi da kuma karairayi, da fuskantar shari’a, ya yanke sharwar daina cin abinci, kuma yana gayyatar dukannin ‘yan siyasar da ke tsare da suma su dauki wannan mataki. 

Ana Sanya ran a yau Litinin ne Ousmane Sonko zai sake gurfana a gaban kotu don amsa wasu tambayoyi.  

Hukuncin shekaru 2 da kotun ta yankewa Sonko a ranar 1 ga watan Yulin da ya gabata ya tayar da tarzoma wadda ta yi sanaddin mutuwar mutane fiye da 20, wanda tuni gamnatin kasar ta alakanta wannan da dan adawa Sonko. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.