Isa ga babban shafi

Kotu ta kawo karshen aure tsakanin Laurent Gbagbo da mai dakinsa Simone Gbabo

Aure tsakanin tsohon shugaban Ivory Coast, Laurent Gbagbo da mai dakinsa Simone Gbabo ya kare a hukumance, kamar yadda tsohon shugaban ya nema jim kadan bayan da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta wanke shi daga zarge-zargen aikata laifukan yaki a watan Yunin shekarar 2021.

Laurent Gbagbo da tsohuwar mai dakinsa Simone Ehivet Gbagbo.
Laurent Gbagbo da tsohuwar mai dakinsa Simone Ehivet Gbagbo. © Photos AFP - Montage RFI
Talla

Labarin mutuwar wannan aure tsakanin Lauren Gbagbo da Simone Gbagbo na kunshe ne a wata sanarwa da lauyar matar, Ange Rodrigue Dadje ya fitar, inda sanarwa ke cewa Mr, Gbagbo  ne silar  wannan tsamin dangantaka sakamakon halin cin amana da rikon sakainar kashi da ya yi wa auren.

Tsohon shugaban na Ivory Coast mai shekaru 78 da tsohuwar mai dakinsa mai shekaru 74, sun bayyana alaka ta aure mai karfi gabanni da kuma  lokacin da ya zama shugaban kasar daga shekarar 2000 zuwa 2011.

Yanzu karewar wannan alaka na nuni da cewa   mata da mijin da suka sha gwagwarmayar assassa tsarin jam’iyyun siyasa fiye da biyu a kasarsu sama da shekaru 30 da suka wuce sun kai gabar da kowa zai kama gabansa, bayan kowannen su ya kafa tasa jam’iyya.

Tare aka kama su a birnin Abidjan a watan Afrilun shekarar 2011 bisa irin rawar da suka taka  a rikicin bayan zaben shugaban kasa da ya yi sanadin mutuwar mutane dubu 3, bayan zaben shugaban kasa na shekarar 2010, wanda Gbagbo  ya ki amincewa da shan kaye a hannun Alassane Ouattara.

Kuma a shekarar 2015, aka yanke musu hukuncin daurin shekaru 20 a gidan kaso kowanne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.