Cutar kwalara ta kashe mutane 5 a Kamaru
Annobar cutar amai da gudawa da ta barke a birnin Younde na Kamaru ta hallaka mutane biyar kawo yanzu, a cewar ma’aikatar lafiyar kasar, wadda kuma tayi gargadi game da daukar matakan kare Yaduwar cutar.
Wallafawa ranar:
Ma’aikatar lafiyar kasar tace a yanzu akwai bayanin mutane 88 dauke da cutar tun farkon watan Maris zuwa yanzu kusan dukannin su a yankin Yaounde na kasar.
Ministan Lafiyar kasar Manouda Malachie ta cikin wata sanarwa da ya fitar, a yanzu dukannin masu ruwa da tsakni a fannin lafiyar kasar na kan shrin ko ta kwana don shawo kan cutar.
A bara dai cutar ta hallaka mutane 272, cikin mutane 12,952 da suka kamu a tsakanin shekara guda kachal.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu