Isa ga babban shafi

Abubuwa biyar da ya kamata a sani game da kasar Kenya

An ayyana mataimakin shugaban kasar William Ruto a matsayin wanda ya lashe zaben, ko da yake wasu daga cikin mambobin hukumar zaben sun ki amincewa da sakamakon, kuma da alama za a ci gaba da fafatawa a kotu.

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta.
Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta. REUTERS - SIPHIWE SIBEKO
Talla

- Karshen mulkin Kenyatta yazo –

Kenya ta samu 'yancin kai daga Biritaniya a ranar 12 ga Disamba, 1963, sakamakon tawayen da Mau Mau suka yi wa mulkin mallaka a tsakanin 1952-1960 wanda ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 10,000.

An nada dan gwagwarmayar samun ‘yancin kai Jomo Kenyatta a matsayin shugaban Kenya na farko bayan mulkin mallaka. Ya rasu a ofis a watan Agustan 1978, wanda mataimakinsa Daniel arap Moi ya gaje shi.

A karshen 1991 Moi ya yi watsi da tsarin mulkin jam'iyya daya kuma ya lashe zaben shugaban kasa a 1992 da 1997.

Daga nan ne Mwai Kibaki ya dare kan karagar mulki a shekara ta 2002 sannan ya sake lashe zaben a shekara ta 2007 inda ya doke Raila Odinga, babban abokin hamayyar Ruto a zaben da aka gudanar a makon jiya.

Takaddamar da aka yi kan kidayar kuri'un da aka kada a shekara ta 2007 ta haifar da tashin hankalin siyasa mafi muni tun bayan samun 'yancin kai, inda aka kashe fiye da mutane 1,100 a rikicin kabilanci.

‘Da ga Jomo Kenyatta wato Uhuru Kenyatta ya doke Odinga a zaben shekara ta 2013 duk da tuhumar da kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta ICC ta yi masa kan haifar da tashin hankalin.

Kotu ta yi watsi da karar da aka shigar a kansa a shekara ta 2014 sannan aka sake zaben Kenyatta a shekara ta 2017, bayan da kotun kolin ta soke nasarar da ya samu a farko, said ai Odinga ya kaurace wa sake zaben zagaye na biyu da aka gudanar.

ICC ta tuhumi Ruto amma masu gabatar da kara sun yi watsi da karar a shekarar 2016.

-Wuraren shakatawa-

Kenya ta ja hankalin maziyarta kusan miliyan 1.5 a bara zuwa wuraren shakatawa na namun daji da rairayin bakin tekun Indiya mai abubuwan ban mamaki.

Daga Maasai Mara zuwa Amboseli, Kenya tana da wuraren shakatawa kusan 50 da wuraren ajiya wadanda ke da gida ga namun daji da suka hada da abin da ake kira Big Five da suka kunshi zakuna, giwaye, karkanda, damisa da buffalo, da rakuma, dorinar ruwa da dangin damisa.

Ruwan da ya taso daga Tanzaniya zuwa Habasha ta hanyar Kenya shi ma wurin yanki ne da aka gudanar da manyan binciken burbushin halittu da ke nuna juyin halittar dan Adam.

An gano gawarwakin mutanen da ake kyautata zaton sun kai kusan shekaru miliyan shida a Kenya.

- Kasar da ke kuryar gabashin Afirka –

Kenya tana da yawan al'ummar Kirista kusan miliyan 50, bisa ga alkaluman gwamnati, wadanda suka kunshi fiye da kabilu 40, mafi girma su ne Kikuyu.

Baya ga kasar Habasha, ita ce kasa mafi karfin tattalin arziki a gabashin Afirka da ke da yawan kudin shiga na cikin gida da ya haura dala biliyan 110 a shekarar 2021, a cewar bankin duniya, kuma ta kasance babbar cibiyar kasuwanci a yankin.

Noma shi ne kashin bayan tattalin arziki kasar, wanda ya kai fiye da kashi biyar na ma’aunin GDP, tare da manyan kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen waje da suka hada da ganyen shayi, da furanni.

Kenya ta kiyasta tattalin arzikinta ya karu da kashi 7.5 cikin dari a bara bayan da ya ragu da kashi 0.3 a shekarar 2020 yayin da annobar Covid-19 ta jefa dubban daruruwan mutane cikin yanayi na rashin aikin yi.

Yanzu haka dai ana fama da matsalar tsadar rayuwa, yayin da farashin man fetur da kayan masarufi suka yi tashin gwauron zabi a kasar da kusan kashi uku na al'ummar kasar ke fama da talauci.

Kenya kuma na fama da matsalar cin hanci da rashawa, inda ta kasance a mataki na 128 daga cikin kasashe 180 na duniya a cikin kididdigar hasashen cin hanci da rashawa ta Transparency International ta shekarar 2021, inda hukumar ta ce yaki da cin hanci da rashawa ya ya tsaya cik.

- Wasan guje-guje da tsalle-tsalle –

Kasar Kenya ta shahara wajen ‘yan wasanta, musamman ‘yan tsere, da ke da tarin lambobin yabo a tarihin gasar cin kofin duniya.

Daga cikin taurarinta da dama akwai wanda ya rike kambun gudun fanfalaki Eliud Kipchoge da Brigid Kosgei da kuma wanda ya fi gudun mita 100 a Afirka, Ferdinand Omanyala.

Duk da haka, wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na Kenya na fafutukar sake farfado da martabar da aka lalata ta hanyar amfani da kwayoyi masu kara kuzari da kuma cin hanci da rashawa.

- Hare-haren ta'addanci –

Kasar Kenya ta sha fama da hare-haren ta'addanci, mafi muni musamman na ranar 7 ga watan Agustan shekarar 1998, lokacin da manyan motocin dakon kaya suka kai hari kan ofishin jakadancin Amurka a Nairobi, inda suka kashe mutane 213 tare da raunata 5,000. Daga bisani Kungiyar Al-Qaeda ta yi ikirarin kai harin.

haka zalika Kenya tana fuskantar hare-hare daga kungiyar Al-Shabaab mai alaka da Al-Qaeda tun a shekarar 2011 wato lokacin da sojojin Kenya suka shiga Somaliya domin yakar masu jihadi.

A watan Satumban shekarar 2013 ne wasu ‘yan bindiga masu ikirarin jihadi suka kai farmaki kan kasuwar Westgate da ke Nairobi, inda suka kashe akalla mutane 67.

A watan Afrilun 2015 wani harin da Al-Shabaab ta kai ya kashe mutane 148 a wata jami'ar Garissa da ke gabashin Kenya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.