El-Rufa'i ya sassauta dokar killace jama'a ta kwanaki 75
Gwamnan Jihar Kaduna da ke Najeriya Malam Nasir El Rufai ya sanar da dokar kawo karshen killace mutane da akayi a gida na kwanaki 75 domin yaki da annobar coronavirus daga gobe laraba.
Wallafawa ranar:
A jawabin da ya yiwa al’ummar kasar ta kafar talabijin, El Rufai ya ce daga gobe laraba dokar hana fita za ta yi aiki ne kawai daga karfe 8 na dare zuwa 5 na asuba, yayin da jama’a za su cigaba da zirga-zirga a cikin Jihar.
Gwamnan ya ce za’a bai wa jama’a damar gudanar da sallar juma’a da addu’a a mujami’u ranakun lahadi kawai, yayin da ake bukatar jama’a su tabbatar da kiyaye dokokin bada tazara wanke hannu da kuma gwajin yanayin jikin mutuum.
El Rufai yace ma’aikata zasu koma bakin aikin su bisa ka’idodin da shugaban ma’aikatan Jihar zai gabatar nan gaba, yayin da za’a dinga bude ofisoshin gwamnati daga karfe 9 na safe zuwa 3 na yamma.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu