Isa ga babban shafi
Najeriya

Hukumar shige da ficen Najeriya ta karbe katin zabe 700 a hannun bakin haure

Babban kwanturolan hukumar shige-da fice a Najeriya, Muhammad Babandede ya sanar da kwace fiye da katinan zabe 700 daga hannun wasu ‘yan kasashen ketare da ke zaune a kasar.

A ranar 16 ga watan Fabarairun sabuwar shekara ta 2019 ne za a gudanar da zaben shugaban kasa a Najeriyar yayinda zaben 'yan majalisu zai biyo bayan sa da makwanni biyu.
A ranar 16 ga watan Fabarairun sabuwar shekara ta 2019 ne za a gudanar da zaben shugaban kasa a Najeriyar yayinda zaben 'yan majalisu zai biyo bayan sa da makwanni biyu. NAN
Talla

A jawaban da ya gabatar yayin wani taron karrama jami’an hukumar da suka yi rawar gani wanda ya gudana yau a Abuja babban birnin Najeriya, Babandede ya ce hukumar na daukar dukkanin matakan da suka dace wajen ganin ‘yan Najeriya ne kadai suka kada kuri’a a zaben shekarar 2019.

Kwnaturolan hukumar ta Shige-da fice ya bada tabbacin cewar hukumar za ta ci gaba da aiki tukuru wajen ganin bakin haure sun tsaya a matsayinsu ba tare da katsalandan a harkokin da suka shafi ‘yan Najeriya kadai ba.

A cewarsa yanzu haka hukumar ta ware wasu jami'ai na musamman da ke aikin tantance bakin hauren da suka mallaki katinan zaben na Najeriya yayinda kuma za su ci gaba da kwacewa don tabbatar da sahihin zabe a kasar.

A ranar 16 ga watan Fabarairun sabuwar shekara ta 2019 ne za a gudanar da zaben shugaban kasa a Najeriyar yayinda zaben 'yan majalisu zai biyo bayan sa da makwanni biyu.

Tuni dai hukumomin da abin ya shafa suka sha alwashin ganin an gudanar da sahihin zabe a Najeriyar, musamman zaben shugaban kasa wanda zai fi jan hankali.

Shugaban kasar Mai ci Muhammadu Buhari ne dai zai fafata da tsohon mataimakin shugaban kasa zamanin Olusegun Obasanjo Atiku Abubakar a zaben na 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.