"Za mu yi sahihin zabe a Zimbabwe saboda marigayi Tsvangirai"
Shugaban Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa ya lashi takobin gudanar da sahihin zabe a kasar don karrama jagoran ‘yan adawa, Morgan Tsvangirai da ya rasu a jiya bayan fama da cutar sankarar hanji.
Wallafawa ranar:
Al’ummar Zimbabwe na cikin alhini saboda mutuwar jagoran ‘yan adawar kasar, Morgan Tsvangirai da ake kallo a matsayin gwarzon da mawuyaci ne a samu tamkarsa a kasar.
Da dama daga cikin mutanen kasar na jinjina wa marigayin saboda rawar da ya taka a gwagwarmayar kafuwar demokradiya a kasar.
Tsvangirai, tsohon jigo a kungiyar ‘yan kwadago, ya kasance babban kalubale ga jam’iyyar ZANU-PF a tsawon mulkinta na kusan shekaru 40.
Shugaba Mnangagwa ya bayyana marigayin a matsayin jajirceccen jagoran ‘yan adawa, sannan kuma ya lashi takobin ganin an gudanar da sahihin zabe kasar a matsayin karramawa ga Tsvangirai da demokradiya.
Mnangagwa ya ce, za a ci gaba da tunawa da marigayin musamman kan nacewarsa ta ganin an gudanar da sahihin zabe.
Tsvangirai ya fuskanci jerin cin zarafi a gwamnatin Robert Mugabe wadda ta garkeme shi a gidan yari.
Morgan Tsvangirai ya rasu ne yana da shekaru 65 da haihuwa bayan fama da cutar sankarar hanji, in da ya yi jinya a wani asbiti da ke kasar Afrika ta Kudu
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu