Isa ga babban shafi
Gambia

Buhari ya samar da zaman lafiya a Gambia- Barrow

Shugaban Gambia Adama Barrow da ke ziyara a Najeriya, ya jinjina wa shugaba Muhammadu Buahri bisa kokarinsa na dakile ruruwar rikicin siyasa bayan Yahya Jammeh ya ki sauka daga karagar mulki.

Shugaban Gambia, Adama Barrow
Shugaban Gambia, Adama Barrow REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Mr. Barrow ya ce, wasu kalamai masu tsauri da Buahari ya furta a yayin wata ganawar sirri a Mali don magance rikicin Gambia, sun taimaka wajen kawo sauyi a kasar.

A yayin taron na Mali, shugaba Buhari ya ce, “Matukar Yahya Jammeh na son kalubalantar yankin yammacin Afrika, to ana marhabin da shi” kamar yadda Barrow ya shaida wa manema labarai a birnin Abuja.

Barrow ya ce, wadannan kalamai na Buhari sun kawo sauyi a Gambia.

A cewar Barrow, ziyararsa na da matukar muhimmanci saboda irin gudun mawar da Najeriya ta bayar wajen tabbatar da tsaro a Gambia.

Jim kadan da sanar da sakamakon zaben shugaban kasa na wancan lokaci, Jammeh ya ki amincewa ya sauka daga karaga don bai wa Barrow damar darewa, har sai da ya sha matsin lamba daga kasashen duniya musamman kasashen yammacin Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.