Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

MDD ta bukaci kare lafiyar jama'a a Juba

Majalisar dinkin duniya ta bukaci kare lafiyar fararen hula da kuma basu damar zirga zirga a Juba da ke kasar Sudan ta kudu, bayan kazamin fadan da aka gwabza da manyan makamai a birnin.

Wasu daga cikin mutanen da suka rasa gidajensu saboda rikicin Sudan ta Kudua  birnin Juba
Wasu daga cikin mutanen da suka rasa gidajensu saboda rikicin Sudan ta Kudua birnin Juba Beatrice Mategwa/United Nations Mission in South Sudan (UNMISS)
Talla

Mai magana da yawun majalisar Alessandra Vellucci ta ce akalla mutane dubu 36  suka rasa matsugunansu kuma suke bukatar inda za su tsuguna a yanzu.

Vellucci ta bukaci a bai wa mutanen da suka samu mafaka a makarantu da majami'u damar samun kayan agaji da suka hada da ruwan sha da magunguna.

Majalisar ta kuma bukaci kasashen da ke makwabtaka da Sudan ta kudu da su bude iyakokinsu don bai wa masu niyyar fita damar samun mafaka.

A bangare guda, hukumar samar da abinci na majalisar dinkin duniya ta ce kashi uku daga cikin hudu na al'ummar kasar  na cikin mawuyacin halin rashin abinci, bayan an kwashe kwanaki hudu ana fama da sabon yakin a kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.