Isa ga babban shafi
Nijar

An kashe jandarmomin Nijar a harin ta'addanci

Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta bayyana cewa, jandarmomin kasar guda 3 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da aka kai kan jami’an tsaro a kusa da kan iyakar Najeriya da Nijar, da kuma wani harin na daban kusa da iyakar kasar da Burkina faso.

Ana zargin kungiyar AQIM da kaddamar da harin Nijar
Ana zargin kungiyar AQIM da kaddamar da harin Nijar
Talla

Wanan dai ya kara nuna yadda matsalar tsaro ke tabarbarewa akan iyakokin kasashen yammacin Afrika da ke fama da hare haren ta’addanci.

Ministan cikin gidan Nijar, Hassimi Massaoudou ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa, wasu ‘yan bindiga da ake zaton mayakan kungiyar AQIM ne suka harbe 'yan sanda uku a wata kasuwa da ke Dolbel kusa da kan iyakar Nijar da Burkina faso.

Minsitan ya ce, an fatattaki mayakan kuma an kashe wasu daga cikinsu, amma sun yi nasarar kwashe gawarwakinsu, abinda ya sa aka kasa san adadin wadanda suka mutu a bangarensu.

A bangare guda, Massaodou ya kara da cewa, wasu 'yan kunar bakin wake guda 4 sun kaddamar da farmaki kan ayarin motocin soji a kusa da kan iyakar Najeriya, inda suka kashe wani kwamanda tare da jikkata wasu sojoji biyu.

Ministan ya ce, kungiyar Boko Haram ce ta kai wannan farmakin na biyu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.