Isa ga babban shafi
Sudan

Kotun Duniya ta bukaci Afirka ta Kudu ta cafke El-Bashir

Kotun hukunta manyan laifufuka a duniya ICC ko kuma CPI ta bukaci hukumomin kasar Afirka ta kudu da su kama shugaban Sudan Umar Hasan El-bashir wanda ke halarar taron shugabannin Afirka yanzu haka a birnin Johannesburg.

Shugaban kasar Sudan Umar Hassan Al Bashir yana kada kuri'arsa.
Shugaban kasar Sudan Umar Hassan Al Bashir yana kada kuri'arsa. REUTERS
Talla

A wani sako da ya fitar a wannan lahadi, Shugaban Kotun ta duniya Sidiki Kaba, ya ce alhaki ya rataya a wuyan hukumomin kasar ta Afirka ta kudu da su cafke El-Bashir sannan kuma su tusa keyarsa zuwa birnin Hague domin ya fuskanci shari’a dangane da laifufukan yaki da na cin zarafin bil’adama da ake zargin sa da aikatawa a Darfur.

Tun shekara ta 2009 ne dai kotun ta fitar da sammanci kasa da kasa domin a kama shugaban na Sudan, lamarin da ya sa ya taikata tafiye-tafiyensa zuwa wasu kasashen duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.