Ebola
An fara amfani da gwajin rigakafin Ebola a Saliyo
Hukumomin Kasar Saliyo sun ce dubban jama’ar kasar za su fara karbar maganin gwaji kan cutar Ebola da ta addabi kasar. Hukumar kula da lafiya a Canada ce ta yi maganin da ake kira RVSV-ZEBOV a karkashin lasisin New Link Genetics da Merck Pharmaceuticals.
Wallafawa ranar:
Talla
Hukumomin sun ce mutane 6,000 za su karbi maganin wanda tuni Cibiyar kula da cututtuka ma su yaduwa na Amurka ta amince da shi.
Cutar Ebola ta kashe mutane sama da 10,000 yawanci a kasashen Liberia da Saliyo da Guinea, tun barkewar cutar a 2013.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu