Isa ga babban shafi
WHO

Hukumar lafiya ta duniya ta gargadi Afrika a kan Ebola

Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta gargadi  hukumomin kasashen Afrika don ganin sun zage dantse tareda bada kulawa da ta dace, wajen yaki da cutar Ebola  

Jami'ar kiwon lafiya na baiwa wata allurar riga kafin Ebola
Jami'ar kiwon lafiya na baiwa wata allurar riga kafin Ebola Reuters/James Giahyue
Talla

Hukumar ta WHO, tayi gargadin ne a lokacin wani taron manema labarai, a birnin Geneva na kasar Swizerland

Shugaban cibiyar yaki da kamuwa da cutar Ebola dake aiki da hukumar lafiya ta Duniya OMS,Dr. Bruce Aylward, ya sanar cewa ana cigaba da bicinken gano allurar kariya da magugunan da suka dace domin yakar cutar ta Ebola a wasu kasshen Afrika.

Dr Aylward ya tabbatar cewa hukumar ba za ta dakatar da bayar da gudumuwa ga kwararun dake cigaba da gudanar da bicinke duk da yake ya zuwa yanzu da sauren aiki a wasu wuraren, ganin yadda mutane ke cigaba da kaucewa bin umurni jami’an kiwon lafiya.

Hukumar lafiya ta Duniya a wani rahoto da ta fitar ta sanar da manufofinta, da suka hada da hanyoyin da suka dace abi domin kiyaye kamuwa da wanan cuta.

A wasu alkaluma da hukumar ta fitar ta sanar da irin yadda aka samu kusan kashi 50 cikin 100 na yawan mutane da suka sake kamuwa da wanan cuta ta Ebola.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.